Zanga-zanga na ci gaba da yin ƙamari a Hong Kong | Labarai | DW | 30.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zanga na ci gaba da yin ƙamari a Hong Kong

Jagoran mulki na Hong Kong Leung Chun Ying ya gargaɗi masu zanga-zangar neman sauye-sauye da su kawo ƙarshen yamutsin da suke yi.

Mista Leung Chun Ying ya yi kira ga jama'a da su gaggauta ficewa daga kan tittunan da suka dadatse cikin ruwan sanhi.Domin kawo ƙarshen cikas ɗin da ake samu a kan sha'anin zirga-zirga, sannan ya ce yana kira ga waɗanda suka shirya wannan zanga-zangar da suka kawo ƙarshenta.

Masu yin yamutsin sun dage cewar za su ci gaba da mamaye tsakiyar birnin na Hong Kong har sai China, ta cikka alƙawarin da ta yi a shekarun 1997 na ƙaddamar da sauye-sauye na siyasa waɗanda za su bai wa al'ummar ta Hong Kong zaɓin shugabanninsu da cikakken yanci.