Zanga zanagar adawa da yakin Iraqi | Labarai | DW | 18.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga zanagar adawa da yakin Iraqi

A ƙasar Australia ɗaruruwan masu adawa da yaƙin da Amurka ke jagoranta a Iraqi suka gudanar da zanga zanga a birnin Sydney yayin cika shekaru uku da afkawa Iraqin da Amurka ta yi. Masu zanga zangar ɗauke da kwalaye da aka yi rubu a cikin su, na kira da a kawo ƙarshen yaƙin sannan Amurka ta gaggauta janye sojojin ta daga Iraqi. Wasu daga cikin kwalayen na ɗauke da kalamai dake baiyana shugaban Amurka George W Bush a matsayin babban ɗan taádda, wasu kuma na ɗauke da bayanai dake baiyana zulumi cewa ƙasar Iran ka iya zama ƙasa ta gaba da Amurka za ta kaiwa mamaye. Adawa da yakin na ƙara bayyana a kasar Australia, wadda ita ma ke da dakarun soji 1,300 a sassan ƙasar Iraqi. Ana tsammanin wasu zanga zangar ta nuna adawa da yaƙin Iraqi a biranen Tokyo da seoul da Kuala Lumpur da London da Madrid da kuma Barcelona.