Zamfara: Boren nuna adawa da hare-haren ′yan bindiga | Siyasa | DW | 21.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zamfara: Boren nuna adawa da hare-haren 'yan bindiga

A jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, mazauna wasu kauyuka sun yi bore domin nuna rashin goyon bayansu ga gwamnatin jihar da jami'an tsaro a kan yadda 'yan bindiga ke ta yi masu kisan gilla.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake kai irin wadannan hare-haren na kisan gilla a jihar Zamfara ba, inda a baya aka sha samun kai hare-hare a yankunan kananan hukumomin Anka da Bukkuyum sai kuma wani da aka kai a karamar hukumar Tsafe. Amma a harin baya-bayan nan da ake zargin barayin shanu da kai wa a wasu kauyuka na karamar hukumar Shinkafi ya yi muni kuma ga shi mahukuntan jihar na kallon abin a matsayin siyasa, kamar yadda wasu mazauna yankin suka yi zargi.

A baya dai sai da hukumomin jihar ta Zamfara suka bayyana yin sulhu da barayin shanun tare da bayyana kawo karshen ayyukansu a jihar, amma kamar yadda mutanen yankin ke cewa sulhun ya zama tamkar daurin gindi ne ga barayin shanun.

Yanzu haka dai mazauna kauyukan da abin ya shafa na gudun hijira ne a wurare kamar Shinkafi da Chanawa da Maberaya da Galadi kazalika da Katuru. Sai dai a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a kaikaice gwamnan jihar ta Zamfara Alhaji Abdul'aziz Yari, ya zargi jami'an tsaro da kasawa, duk kuwa da makudan kudaden suke karba a hannun gwamnatinsa. Ya ce gwamnati ta kashe Naira biliyan 13 a bangaren tsaro a cikin shekaru shida da ya yi a kan karagar mulkin jihar.

Kamin duk wadannnan hare-haren dai sai da maharan suka kona motocin jami'an tsaro guda shida tare da kisan wasu sojin da dama a yankin, abin da mutane da dama ke gani a matsayin kasawar jami'an tsaro. Zuwa yankunan kauyukan da abin ya faru dai na cike da hatsari.

Sauti da bidiyo akan labarin