Zambar bakin haure ta wargaje a Turkiya | Labarai | DW | 28.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zambar bakin haure ta wargaje a Turkiya

'Yan sanda a kasar Turkiya sun kubutar da wasu 'yan gudun hijira 'yan asalin Pakistan su 57 wadanda aka boyesu a wani waje daure cikin sarka.

Wata kafar yada labarai a Turkiya ta bada wannan labari a wannan rana ta Talata in da ta ce wasu masu fasakaurin jama'a dubunsu ta cika. Masu fasakaurin dai sun fadawa mutanen za su kaisu kasahen Turai idan suka hada musu Dalar Amirka dubu goma, kuma a cewar rahoton kafar yada labaran ta Turkiya an daure mutanen inda aka bukaci su kira 'yan uwansu a gida su zuba kudi a wani asusun banki na masu fasakaurin bayan sun fadawa 'yan uwan nasu cewa tuni sun isa Turai.

Kafar yada labaran ta Hurriyet ta ce tuni 'yan sanda suka kama mutane uku daga cikin masu fasakaurin wadanda su ma 'yan asalin Pakistan ne bisa zarginsu da aikata ta'asa da bawa mutanen bayanan karya na cewa za su kaisu Turai ta hanyar ratsa Girka da Italiya