Zamba a cikin watan Azumin Ramadan | Zamantakewa | DW | 06.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Zamba a cikin watan Azumin Ramadan

A jihar Sakkwato da ke arewacin Najeriya ana zargin wasu mutane da gwamnatin jihar ta damka wa amanar ciyar da mabukata a lokutan buda baki da karkata akalar kayan abincin da aka ba su don biyan bukatun gidajensu.

Bisa al'ada dai ko wacce shekara gwamnatin jihar Sakkwato kan ware makudan kudade domin wannan aikin na bai wa mabukata abincin buda baki. Sama da Naira miliyan 300 ne gwamnatin jihar ta ware domin ciyar da mabukata abincin buda baki a wannan shekarar kawai, wanda ake rarraba abinci a kusan cibiyoyi 311. To sai dai a wani abin da masu lura da al'amura ke bayyanawa sun ce, wasu daga cikin wadanda aka damkawa amanar suna yin gaban kansu ne kawai wajen karkata abincin zuwa gidajensu. Hakan dai na zaman wani abin takaici daf da lokacin da ake ciki na watan mai alfarma wanda ake neman gafara a cikinsa.