ZAINAB AMJ ABUBAKAR | Siyasa | DW | 03.11.2003
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

ZAINAB AMJ ABUBAKAR

Wani Rahoto da mujallar Wall Street Jonal ta Amurka ta wallafa na nuni dacewa kalubalantar manufofin gwamnatin Amurka akan Iraki da Mr Kofi Annan ya fito karara yanayi,ya tabbatar da dacewa shugaban hukumar sulhunta duniyan na adawa ne da gwamnatin Bush fiye da gwamnatin Sadam Hussein da aka rusa.
A ranar Alhamis data gabatane sakataren Mdd ya sanar da janye jamiansa daga Birnin Bagadaza dangane da abunda ya kira rashin tsaro.A lokacin da Annan yace kudurin Amurkan ya gaza fayyace wasu batutuwa dangane da Iraki,wani jamiin Amurka wanda baa ambaci sunansa ba kuma ake zargin cewa sakataren harkokin wajen Amurka Colin Powel ne,yace furucin na Annan ba zai haifar da komai ba face tashin hankali.
A jawabinsa na kaddamar da taron koli na majalisar a watan Satumba,Annan yayi Allah wadan harin da bashi da dalili,kamar yadda Amurka ta Afkawa Iraki ba tare da amincewan MDD.Kazalika a wani taro na musamman dangane da yaki da taadanci a watan Satumba,Sakataren na MDD,ya laanci taadancin kasa da kasa ,wanda yake nufin abunda Izraela ke aikatawa.
Wadannan kalamai na Mr Annan dai ya jima da samun suka musamman daga manazarta na Amurka,wadanda ke ganin cewa gwamnatin Amurka batayi laakari dacewa wannan mataki da take dauka nada Illoli wa hukumar da Annan kewa jagoranci ba.Bugu da kari Kofi Annan ya gano cewa barin gwamnatin Bush tana cin karen ta babu babbaka zai zubar da darajar MDD a idanun duniya.
Galibi ma dai masu lura da alamura dakaje suzo na ganin cewa Shugabannin hukuma kamar mdd basa wuce rike wannan matsayi sau biyu,amma Annan ya kasance daya daga cikin mutanen da alumma ke ganin kimarsu.
Annan dan kasar Ghana,kana mutumin Afrika na farko daya riki wannan mukamin,zai kammala zagayen shugabancinsa na shekaru biyar na biyu a watan Disamban shekara ta 2006.
Masharhanta na ganin Annan a matsayin namijin duniya wajen kalubalantar Amurka,kamar yadda yake tin karan wasu kasashe masu tasowa,idan kuwa baiyi haka ba to ba shakka tarihi bazai barshi a baya ba wajen bayyanar dashi da kasancewa shugaban MDD daya kasa kare hukumar dayake jagoranta.
To sai dai bayan Shugaba Bush ya sanar da kawo karshen yakin na Iraki,Annan yayi kira ga kasashen duniya dasu taimakawa kasar ta Iraki wajen farfado da ita bayan yaki.