1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zafin rana ya kai kololuwa a kasashen Turai

Mouhamadou Awal Balarabe
July 19, 2022

Faransa ta fuskanci zafin rana da ba ta taba ganin irinsa ba a tarihinta sakamakon sauyin yanayi. Su ma kasashen yammacin Turai suna fama da rana mai tsanani da matsalar wutar daji.

https://p.dw.com/p/4ENdK
Hitzewelle in Spanien
Hoto: Ricardo Rubio/EUROPA PRESS/dpa/picture alliance

Kasar Faransa ta fuskanci yanayin tsananin zafi da ba ta taba gani ba a tarihinta, inda hukumar da ke kula da hasashen yanayi ta ce zafin ya kai maki 42.6 ° a ma'aunin Celcius a wasu kananan hukumomi da ke kewayen Paris. Tun a jiya Litinin ne zafin rana ya fara kaiwa kololuwa a wasu kananan hukumomi 64 na kasar Faransa da Ingila da Spain, lamarin da ke haddasa gobarar daji a wasu yankuna.

A kasar Birtaniya, hukumomi suka ce yanayin zafin yakai maki 40 a ma'aunin celcius, bayan maki 38 a aka fara kaiwa a gabashin kasar. Tuni aka fara kwantar da gajiyoyi a asibitoci sakamakon hali da tsananin zafi ya jefa su a ciki. A daya hannun kuma matsalar wutar daji da ta kunno kai sakamakon zafin na addabar kasashen Girka da Portugal da Spaniya da ma wani bangare na kasar Faransa.

Hukumomin Turai na danganta wannan tsananin zafin rana da matsalar ta dumamar yanayi.