Zabukan gwamnoni a jihohin Bayelsa da Kogi | Siyasa | DW | 05.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zabukan gwamnoni a jihohin Bayelsa da Kogi

Rikici ya barke a wasu yankuna na jihar Bayelsa, lokacin da wasu 'yan bindiga suka bude wuta akan masu kada kuri'a wanda ya jagoranci asarar rayuka.

Ya zuwa yanzu dai akwai rahotanni da ke nuni da cewar an samu asarar rayuka, a yayin da mutane da dama suka ki fita saboda razana da suka yi dangane da yiwuwar tashin hankali. Tun a baya dai kungiyar MEND da ke fafukata a yankin na Niger Delta ta yi alkawarin tura 'ya'yanta 500 zuwa sassan gudanar da zaben.

Wakilin DW da ke yankin ya ce jami'an tsaro sun gaza zuwa wuraren da ake samun rigingimu, duk da alkawarin da rundunar 'yan sanda ta yi na samar da tsaro.

Gabannin fara zaben dai an samu yamutsi tsakanin magoya bayan gwamnat mai ci wanda ke neman tazarce a jam'iyyar PDP Seriake Dickson da na abokin takararsa na jam'iyyar APC Timipre Sylva, da ke zama tsohon gwamnan jihar.

Sauti da bidiyo akan labarin