1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Saliyo ya dau hankalin jaridun Jamus

Mohammad Nasiru Awal
March 30, 2018

A zagaye na farko na zaben shugaban kasa a Saliyo kimanin kashi 84 cikin 100 na wadanda suka cancanci kada kuri'a suka yi zabe to amma kasancewa ba dan takarar da ya samu yawan kuri'un da ake bukata za ai zagaye na biyu.

https://p.dw.com/p/2vFux
Wahlen in Sierra Leone  2018
Hoto: DW/A.-B. Jalloh

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce duk wanda ya yi nasara a zaben ya kuma zama sabon shugaban kasar ta Saliyo to akwai babban kalubale a gaban shi. Kasar dai daya ce a jerin kasashe mafi fama da matsalar talauci a nahiyar Afirka. Daga shekarar 1991 zuwa 2002 ta yi fama da yakin basasa da ya yi sanadin rayukan mutane kusa dubu 200. A shekarun bayan nan kuma ta fuskanci annobar cutar Ebola sannan a watanni baya wata zaftarewar kasa sakamakon ruwan sama mai karfi a birnin Freetown ta kashe mutum fiye da dubu daya.

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung ta yi tsokaci ne kan zaben 'yan majalisar dattawan kasar Cote d'Ivoire da ya gudana a karshen mako. Ta ce a zaben na 'yan majalisar dattawa ya fito fili yadda har yanzu ake fama da rarrabuwar kai a kasar shekaru bakwai bayan kawo karshen yaki ba bu wanda ke son ya yi magana game da rikicin.

Daga watan Disamban 2010 zuwa watan Afrilu na 2011 fiye da mutane dubu 3 ne suka rasa rayukansu sakamakon mummunan rikici a kasar ta Cote d'Ivoire biyo bayan zagaye na biyu na zaben shugaban kasa. Shugaban kasa na wancan lokaci Laurent Ggagbo ya ki amincewa da kayen da ya sha a hannu mai kalubalantarsa Allasane Ouattara. Jaridar ta ruwaito wasu 'yan kasar na cewa har yanzu rikicin na da babban tasiri a rayuwar al'ummar kasar da ma a fagen siyasa. Wata babbar matsalar ma dai ita ce rashin wata tattaunawa don samun mafita tsakanin gwamnati da 'yan adawa.