Zaben mambobin Kwamitin Sulhun MDD | Labarai | DW | 12.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben mambobin Kwamitin Sulhun MDD

Jamus ta sami wakilcin kujerar karba-karba a Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya

default

Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya

Jamus ta yi nasarar samun kujerar karba-karba na wa´adin shekaru biyu a kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya. Wannan ya biyo bayan wani ƙuri'ar da mambobin kasashe192 da ke babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya su ka kaɗa ne yau a birnin New York.

Baya ga mambobin kasashe biyar masu dauwamammiyar kujera a hukumar, akwai sauran kujeru 10 da ake bai wa sauran kasashe wakilcin karba-karba.

A yanzu dai, Jamus za ta bi sahun ƙasashen Afirka ta kudu da Kolombiya wadanda suka sami wakilci daga shekarar 2011 zuwa 2012 a Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniyar. Ana sa ran tantance ƙasar da za ta ɗauki kujera ta ƙarshe tsakanin ƙasashen Portugal da Kanada bayan an gudanar da zaɓe zagaye na biyu.

Mawallafiya: Pinado Abdu

Edita: Abdullahi Tanko Bala