Zaben kasar Cape Verde. | Siyasa | DW | 21.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaben kasar Cape Verde.

A ran lahadi, 22 ga watan Janairu ne ake gudanad da zabe a kasar Cape Verde. Hasashe dai na nuna cewa, babu wata jam'iyyar da ta shiga takarar zaben, da ke nuna alamun samun cikakken rinjayi. Sai dai a jira a ga yadda sakamakon zai kasance.

A yakin neman zaben da aka gudanar a kan tsibirin Cape Verde dai, duk jam’iyyun kasar sun fi mai da hankalinsu ne kan inganta huldodinsu da sauran kasashen nahiyar Afirka, musamman ma dai kungiyar tattalin kasashen Afirka Ta Yamma, ko kuma ECOWAS a takaice.

Jam’iyyar PAICV, wadda ke jan ragamar mulkin Cape Verde din a halin yanzu, ta ce burinta ne ta jagoranci kasar wajen kasancewa kofar shigowa nahiyar Afirka ta ruwa. Tsibiran na Cape Verde dai na da muhimmanci kwarai, saboda kasancewarsu a tsakiyar tekun Altlantik, inda jiragen ruwa ke bi daga nahiyar Afirka zuwa Turai. Bugu da kari kuma, jam’iyyar ta lashi takobin yakan talauci da kuma ci gaba da bunkasa tattalin arzikin kasar, idan ta lashe zaben da za gudanar yau. Kamar yadda shugabanta da kuma Firamiyan kasar, Maria Neves ya bayyanar:-

„Muna son inganta bunkasar tattalin arzikinmu don mu sami amincewa a ketare. Ta hakan ne kuma za mu iya janyo hankullan masu zuba jari zuwa kasarmu. Kazalika kuma, za mu fadada fannonin tattalin arzikinmu da masana’antu da kamfanoni don samad da guraban aikin yi ga jama’a, su ma su iya inganta halin rayuwarsu.“

Tun cikin watan Yunin shekara ta 2000 ne José Maria Neves ke jagorancin jam’iyyar ta PAICV. Ya gaji mukamin ne daga Pedro Pires, wanda a halin yanzu shi ne shugaban kasa. Shi dai Maria Neves, mai shekaru 47 da haihuwa, ya yi karantunsa na fannin tattalin masana’antu ne ne a kasar Brazil. Amma yana ganin kansa ne tamkar daya daga cikin talakawn kasar. Kamar yadda ya bayyanar:-

„Ina ganin kai na ne kamar dan kasar Cape Verde, wanda yake kishin kasarsa yake son kuma ya bauta mata. Ta hakan ne dai nake son gabatar da kaina ga sauran `yan kasarmu, kuma bisa wannan maufar ne nake son in ci gaba da aikina.“

To, amma dai kafin ya iya ci gaba da aikinsa, sai ya doke jam’iyyar adawa ta MpD a zaben na yau. Duk da cewa ita jam’iyyar adawar ta fi karkata zuwa bangaren `yan mazan jiya ne, yayin da jam’iyyar PAICV mai jan ragamar mulki kuma ke bin kaidar `yann gurguzu, manufofin jam’iyyun biyu dai ba su wani bambanci. Ita ma jam’iyyar MpD din, ta ce burinta ne ta bunkasa harkokin ilimi a kasar, sa’annan kuma ta samar wa matasa guraban ayyukan yi. Abin da dai ya ba kowa mamaki ne, kiran da jam’iyyar ta yi na sake nazarin kasancewar kasar cikin kungiyar tattalin arzikin kasashen Afirka Ta Yamma. Akwai wani bangare na `yan kasar da ke koke-koken cewa, shigowar jama’a da dama daga kasashen Afirka Ta Yamma cikin Cape Verde din ne ya habaka yawan masu aikata laifuffuka da kuma masu cinikin miyagun kwayoyi. Bugu da kari kuma, suna ganin, masu jigilar bakin haure zuwa Turai daga Afirka Ta Yamma, na ta kara amfani ne da tsibirin. Shugaban jam’iyyar ta MpD, António Lopes, wanda ya yi karatun injiniya a kasar Aljeriya, ya bayyana cewa:-

„Ni dai dan siyasa ne, maras girman kai, wanda kuma na fi ba da fiffiko ga aikin gayya. Saboda mutum daya kawai, ba zai iya magance matsalolin da muke huskanta a nan kasar ba. Idan ko ba mu sami mutanen da za mu iya yin aikin gayya da su tare ba, to ba za mu iya shawo kan matsalolin kasarmu ba. A namu bangaren dai, mun yi imanin cewa mun ada wasu kyawawan shawarwari na tinkarar matsalolin da kasarmu ke huskanta. Ina son dai in jagoranci wannan rukuni na aikin gayya, wanda zai iya sake alkiblar kasarmu.“

Kawo yanzu dai, mahukuntan kasar, sun cim ma nasarar aiwatad da manufofi da dama don inganta halin rayuwar `yan kasar, wadanda yawansu ya kai rabin miliyan. Kuadaden shigar da kasar ke samu a shekara, za su iya tabbatar wa ko wane dan kasar samun dola dubu 6 da dari 2, idan da za a rarraba su ne ga duk jama’a. Hakan kuwa ya zo daidai da matsyin da ake da shi a kasashen Sin, da Jumhuriyar Dominican da kuma Venezuela. Amma duk da haka, an kiyasci cewa kusan kashi 37 cikin dari na al’umman kasar ne ke fama da talauci. Gwamnatin kasar dai ta dukufa ne wajen inganta fannnin yawon shakatawa, saboda tana ganin nan gaba, wannan fannin zai iya zamaowa wani muhimmin tushe na samad da karin kudaden shiga.