Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
An gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki a Ghana, zaben da shugaba mai ci Nana Akufo-Addo ya samu wa'adi na biyu na mulki.
Hukumar zaben Ghana ta bayyana Nana Akufo-Addo a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da ya gudana a ranar Litinin. Dama ta bayyana sakamakon zabe 'yan majalisar dokokin na sassan kasar.
A yayin da Hukumar zabe EC ke baiyana sakamakon zabe na kananan mazabu, dan takaran jam'iyya NDC mai Mulki kuma mai neman yin tazarce, Shugaba Nana Akufo-Addo na ikirarin cewa shi ne kan gaba a zaben.
Hukumar zaben Ghana na ci gaba da tattara sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi a jiya Litinin inda takara ta fi zafi tsakanin shugaba mai ci Nana Akufo-Addo na NPP da tsohon shugaban kasar John Dramani Mahama na NDC.
Rayukan mutane biyar sun salwanta a tashe-tashen hankula masu nasaba da zabe a yankunan kasar Ghana a yayin da wasu 17 suka ji rauni.
'Yan takarar shugaban kasa a manyan jam'iyyun siyasa biyu NPP da NDC sun amince da yin zaben cikin lumana, yayin cimma yarjejeniyar zaman lafiya da suka rattaba hannu akai a Accra.
Akasarin jam'iyyun siyasar kasar Mali sun yi watsi da wa'adin mika mulki na shekaru biyar da gwamnatin mulkin soja ta gabatar ga kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS KO CEDEAO.