Rikicin zabe ya halaka mutane a Ghana | Labarai | DW | 09.12.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin zabe ya halaka mutane a Ghana

Rayukan mutane biyar sun salwanta a tashe-tashen hankula masu nasaba da zabe a yankunan kasar Ghana a yayin da wasu 17 suka ji rauni.

Hukumar 'yan sandar Ghana ta ce an fuskanci rigingimu masu nasaba da zaben har sau 21 a sassa da dama na kasar, lamarin da ya haddasa kisan mutun biyar da raunata wasu 17.

Yanzu haka hankulan 'yan adawa da na masu mulki sun raja'a kan hukumar zaben kasar a ci gaba da dakon cikakken sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin da suka gabata.

Tuni sakamakon yankuna bakwai a cikin 16 na kasar ya nuna madugun adawa John Mahama  na kan gaba da abokin fafatawarsa Nana Akufo-Addo.