John Dramani Mahama shugaban kasar Ghana, kana stohon mataimakin shugaban kasa wanda ya dauki mulki sakamakon rasuwar Shugaba John Atta Mills.
Mahama ya rike mukamai daban-daban kafin ya zama shugaban kasa da suka hada da zama dan majalisa, da rike mukamun minista, sannan mataimakin shugaban kasa.