Zaben Amirka: Fargabar Magudi | Labarai | DW | 02.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben Amirka: Fargabar Magudi

Dan takarar jam'iyyar Republican Donal Trump ya bayyana abokiyar takararsa Hillary Clinton a matsayin "shedaniya" inda ya ke fargabar a tabka magudi a babban zaben Amirka da ke tafe.

Dan takarar shugabancin Amirka a karkashin jam'iyyar Republican Donal Trump ya bayyana fargabar afkuwar magudi a babban zaben da zai gudana a watan Nuwamba. Trump ya kuma bayyana abokiyar takararsa, Hillary Clinton da Sanata Berni Sanders a matsayin "shedanu". Trump ya bayyana wadannan kalamai ne a bainar magoya bayansa yayin gudanar da gangamin yakin neman zabe a Clombus.

To sai dai dan takarar bai gabatar da kwararran hujjoji a kan zargin da yake ganin zaben zai fuskanci tangarda na aringizon kuri'u ba, to sai dai wasu sanatoci masu ra'ayin mazan jiya a jam'yyar ta Rebublican sun soki lamirin dan takarar Donal Trump a kan martanin da yayi wa iyalan Sojan nan dan Amirka da ya rasa ransa a fagen dagga a Iraki shekaru 17 da suka gabata.