Zaben 2019: INEC na da jan aiki a gabanta | BATUTUWA | DW | 21.02.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Najeriya: Hukumar INEC na da jan aiki a gabanta

Zaben 2019: INEC na da jan aiki a gabanta

Gamayyar kungiyoyin kare hakkin jama’a a Najeriya sun bayyana cewa har yanzu akwai sauran aiki a gaban hukumar zaben kasar game da shirye-shiryen zaben na ranar asabar.

Kungiyoin fara hula da ke sa ido a kan zaben na Najeriya sun yi waiwayen halin da ake ciki musamman shirye-shiryen da hukumar zaben ke yi wanda suka ce duk da kamalla sake daidaita naurar tantance katin masu jefa kuri’a wato card reader da kuma aikin kai kayan zaben zuwa jihohi.

Farfesa Nuhu Yakubu daya ne daga cikin jami’an gamaiyyar kungiyoyin  farar hular ta Najeriya, yace har yanzu akwai batun samun kayan wasu jihohi a wasu jihohi da ke zama babban kalubalen da ya kamata a shawo kansa don kaucewa fuskantar koma baya.

Kungiyoyin dai sun bayyana fargaba kan yanayin tsaro da za’a iya fuskanta a zaben musamman bisa abubuwan da suka faru bayan soke zaben a  makon da ya gabata da kuma sauya wa kwamishinonin ‘yan sanda na jihohin Zamfara da Kano da Akwa Ibom wuraren aiki.

A yayinda hukumar zaben ke shirin fara horar da ma’aikata wucin gadi, kungiyoyin farar hula na nuna damuwa a kan ingancinsu da ma yadda aka gaza samar masu muhalli mai kyau a lokacin zaben da aka dakatar.

Duk da shirin da bayanin da hukumar zaben ta INEC tace ta yi, jama’a na nuna shakku game da zaben kansa abinda kwararru suka ce zai shafi yawan mutanen da za su fito don yin zaben.

 

Sauti da bidiyo akan labarin