Zabe cikin rashin tabbas a Burundi | Siyasa | DW | 29.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zabe cikin rashin tabbas a Burundi

An bude tashoshin kada kuri'a a zaben 'yan majalisa da kananan hukumomi a kasar Burundi ba al'umma sosai da suka fito kada kuri'a, bayan jefa makaman gurneti a wasu mazabu.

Parlamentswahlen in Burundi

Masu kada kuri'a da jami'an tsaro na zabe a Burundi

Wasu da ba a san ko suwaye ba sun jefa makaman gurneti a wasu mazabun da aka tanada dan kada kuri'a a birnin Bujumbura da ma wasu tashoshin da a ka tanada a wasu kananan hukumomi, abin da ya sanya ba a fara zabukan 'yan majalisar dokoki da wuri ba a wasu sassan a ranar Litinin din nan kamar yadda jami'an 'yan sanda suka nunar.

Ko da a ranar Litinin din ma dai sai da wani makamin gurnetin ya tashi a birnin na Bujumbura fadar gwamnatin kasar ta Burundi, wani abu na baya-bayan nan da ke nuna kara ta'azzara da adawa da shirin shugaba Nkrunziza na neman tazarce karo na uku.

Parlamentswahlen in Burundi

Jami'an tsaro na jiran masu zabe

A dai wuraren da rikicin ya fi kamari tulin jami'an tsaro ne soja da 'yan sanda ake gani sai daidaikun fararen hula da suka hau layi dan kada kuri'a mai cike da burin samar da zaman lafiya a kasar kamar yadda Elias Niyoyitungira ke cewa :

"Ina fatan mutanen da zamu zaba su zama masu yi wa al'umma aiki, ina so su maido mana da zaman lafiya, su kuma jagoranci kasar ta yadda za ta sami ci gaba."

Hukumar zaben kasar dai na ikirarin fitowar masu kada kuri'a da dama sai dai a wasu wuraren ba haka yake ba kasancewar mutanen wurarenma sunyi kaura.

Tun dai bayan da kasar ta tsinci kai a yanayi na tashin hankali al'umma ke ta ficewa daga wannan kasa saboda fargabar abin da ka je ya dawo musamman abin da ake tsammani bayan zaben kasar da ake ganin lamura za su kazance. A ci gaba da samun tudadar 'yan gudun hijira a kasashe makwabta da adadinsu ya kai 127,000 da ke watse a kasashen Ruwanda da Tanzaniya da Yuganda da Jamhuriyar Demokradiyar Kwango da Zambiya ban da wadanda ba su yi rijista ba.

Flüchtlinge in Burundi

'Yan gudun hijira na ficewa daga Burundi

A cewar Adrian Edwards, da ke magana da yawun ofishin 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniyar gabannin wannan zabe na Burundi suna kara ganin yawaitar masu neman mafaka a wadannan kasashe:

"Ofisoshinmu a kasashen da ke kusa da Burundi na lura da karuwar 'yan gudun hijira, mutane na fada mana cewa suna tsoro ne kar rikici mai nasaba da siyasa da kasar za ta iya fadawa ko a rika kai musu hari da makamai koma a rika kamasu"

Shi ma dai shugaban majalisar dokokin kasar Pie Ntavyohanyuma ya tsallake daga kasar zuwa Belgium saboda neman tsira da rayuwarsa a cewarsa, sakamakon nuna adawarsa da shirin tazarcen shugaba Nkrunziza da ya bayyana takararsa da cewa haramtacciya ce shi ya sa ya dau wannan mataki:

" Ina so na fada masa cewa shirinsa na neman tazarce bai halatta ba, ina fada masa cewa kutsa kai dan neman a zabe shi ta karbi abu ne da ya sabawa hankali ."

Tun dai a makon jiya ne Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya bukaci a dage wannan zabe da aka fara a ranar Litinin din nan baya ga kungiyar kasashen Turai da ta bayyana zaben a matsayin mataki na kara kai mutane kaburbura da kara dagula lamura a kasar, sannan ta sake jadada janye tallafin da ta ke ba wa Burundi saboda rashin mutunta muradun Majalisar Dinkin Duniya. Ita ko kungiyar AU cewa ta yi ba da hannunta ba a sanya idanu a zaben 'yan majalisar da ba ta da tabbaci a makomar sahihancinsa.

Sauti da bidiyo akan labarin