Zabe a Burundi da bullar cutar Ebola a Liberiya | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 03.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Zabe a Burundi da bullar cutar Ebola a Liberiya

Zaben majalisar dokoki a Burundi mai cike da rudani da sake bullar cutar Ebola a Liberiya sun dauki hankalin jaridun Jamus a wannan mako.

A sharhin da ta yi jaridar Süddeutsche Zeitung cewa ta yi a Burundi shugaban kasa Pierre Nkurunziza ya bari an gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki mai cike da rudani. Ya kuma yi haka duk da jerin zanga-zangogi da tashe-tashen hankula da kuma kaurace wa zaben da 'yan adawa suka yi. Bugu da karin dubun dubatan 'yan Burundi ciki har da mataimakin shugaban kasa na biyu da kuma kakakin majalisar dokoki, sun tsere daga kasar. Jaridar ta kara da cewa kasar ta Burundi na kara tsunduma cikin rikici tun a karshen watan Afrilu lokacin da jam'iyyar Shugaba Nkurunziza ta sake tsayar da shi a matsayin dan takararta a zaben shugaban kasar da zai gudana a tsakiyar wannan wata na Yuli, duk da haramcin yin haka karkashin kundin tsarin mulkin kasar.

Biris da matsin lamba

Zabe a Burundi cikin yanayi na tarzoma inji jaridar Neue Zürcher Zeitung tana mai cewa Shugaba Nkurunziza ya yi kunnen kashi ga masu sukar lamirinsa.

Burundi Präsident

Shugaba Pierre Nkurunziza ya yi biris da matsin lamba na ciki da wajen Burundi

Ta ce an gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki a Burundi kasar da tun cikin watan Afrilu ke fama da tashe-tashen hankula. Ta ce rikicin siyasar kasar ya ta'azzara tun farkon shekara sakamakon yunkurin Shugaba Nkurunziza na neman wa'adin mulki karo na uku sabanin tanade-tanaden dokokin kasar. Sai dai bisa ga dukkan alamu shugaban ya yi kunnen uwar shegu da matsin lamba na ciki da wajen kasar. Idan ba a yi hattara ba Burundi ka iya zama wata kasar Afirka ta gaba da rikici za su dabaibaye ta.

Ebola ta sake bulla a Liberiya

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung labari ta buga game da sake bullar cutar Ebola a kasar Liberiya.

Sierra Leone Ebola

Ebola ta sake bulla a Liberiya har ma ta kashe wani matashi

Ta ce makonni bakwai bayan da a hukumance aka ayyana samun nasarar magance annobar Ebola a Liberiya, abin da kuma ya kawo karshen cutar a kasar, wani matashi dan kasar mai shekaru 17 ya mutu sakamakon kamuwa da kwayoyin cutar. Ba a dai san yadda ya harbu da cutar ba, domin a cewar ma'aikatar kiwon lafiya matashin da ya fito daga wani yanki mai tazarar kilomita 50 daga Monroviya babban birnin kasar, ya kwashe makonni da dama bai bar yankin na su ba. Cutar Ebola da ta barke a karshen shekarar 2013 a wasu kasashen Afirka ta Yamma, ita ce mafi muni tun gano kwayoyin cutar a kungurmin dajin Kwango a shekarar 1976. Cutar ta hallaka mutanee fiye da 1100 a kasashen Guinea da Liberiya da kuma Saliyo.

Rage yawan matsalar yunwa a duniya

Ana iya magance matsalar yunwa inji jaridar Die Welt tana mai cewa duk da bunkasar yawan al'umma da aka samu a duniya a cikin shekaru 25 da suka gabata, an samu nasarar rage yawan masu fama da matsalar yunwa da kashi 50 cikin 100 a tsukin wannan lokaci. Ko da yake abubuwa da yawa ke janyo matsalar yunwa, amma fa idan aka dauki matakan da suka dace a lokacin da suka dace da kuma wuraren da suka fi dacewa, ana iya shawo kanta.