1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a yi bincike kan Cutar Ebola a Kwango

October 15, 2018

Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ce za ta aike da kwararrunta zuwa Kwango don tantance ko cutar nan ta Ebola da ta bulla a kasar ta shiga matsayin matsalolin gaggawa na lafiya a duniya.

https://p.dw.com/p/36atN
Kongo Ebola
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Bompengo

Kwararrun za su isa Kwangon ne kan batun a Larabar da ke tafe don tababatar da girman barazanar da ta halaka mutum 135 a arewacin yankin Kivu daga watan Agusta zuwa yau.

Cutukan da ake bayyana su a matsayin matsalolin gaggawa dai su ne wadanda aka hakikance cewa suna iya ratsa iyakoki cikin hanzari, da kuma ke bukatar matakin kasashen duniya a gaggauce.

A shekara ta 2014 ma an bayyana Ebolar a wannan matsayin lokacin da ta halaka dubban rayuka a wasu kasashen Afirka ta Yamma kamar yadda aka bayyana cutar Zika a shekara ta 2016.