Za a rantsar da Mohammadu Buhari
May 29, 2015Talla
Nan gaba a yau aka shirya ƙaddamar da bikin rantsar da sabon shugaban ƙasar Najeriya Mohammadu Buhari,bayan nasarar da ya samu a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a cikin watan Maris da ya gabata a gaban shugaban mai bari gado Goodlluck Jonathan.
An shirya shugabannin daga ƙasashen Yankin Afirka da Turai da Asiya da kuma na manyan ƙungiyoyi za su halarci bikin.