Za a fara bincike kan kisan da ake yi a arewacin Najeriya | Labarai | DW | 11.12.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a fara bincike kan kisan da ake yi a arewacin Najeriya

Kotun binciken manyan laifuffuka ta ICC ta ce ta mallaki shedu da dama kan kashe-kashen da 'yan kungiyar Boko Haram ke yi a Najeriya.

Babbar mai shigar da kara a kotun hukunta masu aikata manyan laifuffuka ta kasa da kasa wato ICC Fatou Bensouda, ta ce tana da cikakkiyar shedar fara bincike kan kashe-kashen da masu ikirarin jihadi ke yi a arewa maso gabacin Najeriya.

Mai shigar da karar ta kara da cewa shedun da ke gareta a hannu, sun isa a bude bincike kan abin da ke gudana a yankin na arewacin kasar.

Kungiyar Boko Haram ta kwashe sama da shekaru goma tana kisan farar hula da basu ji ba basu gani ba a jihohin Barno da Yobe.

Yankin arewacin na Najeriya na cigaba da fuskantar hare-haren 'yan ta'ada da masu garkuwa da mutane.