Za a cigaba da zanga-zanga a Burundi | Labarai | DW | 27.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a cigaba da zanga-zanga a Burundi

Kungiyoyin fararen hula sun bukaci al'ummar Burundi da su cigaba da zanga-zanga a yau don nuna kyamarsu da yin tazarce da shugaban kasar ke son yi.

A wannan Litinin din, kungiyoyin fararen hula da ke jagorantar adawa da tazarcen Shugaba Nkurunziza sun bukaci da a fantsama kan titunan birnin Bujumbura yayin da suka nemi 'Yan kasuwa da su kauracewa shagunansu kana suka bukaci iyaye da kada su tura yaransu makaranta a wani mataki na nuna rahsin amincewar da koakrin kankane gadon mulki da Nkurunziza ke son yi.

Kamfanin dilancin labaran na Faransa AFP ya ambato shugaban ƙungiyar masu gidajen rediyion Patrick Nduwimana na mai cewar gwamnatin ta dakatar da shirye-shiryen saboda zargin da ta ke yi musu na tunzura jama'a wajen tayar da ƙayar baya, abin da ya ce ba gaskiya ba ne.

A jiya Lahadi dai an samu asarar rai bayan da 'yan sanda a kasar su ka yi artabu da wasu ɗarurruwan jama'ar da suka yi zanga-zanga a birnin Bujumbura, domin nuna ƙin amincewa da takarar shugaba Pierre Nkurunziza a zaɓen shugaban ƙasar a wa'adi na uku, lamarin da ya yi sanadin rasuwar mutane biyu.