Zaɓen gwamnoni a jihohin Bayelsa da Kogi | Siyasa | DW | 06.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaɓen gwamnoni a jihohin Bayelsa da Kogi

Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta fara raraba katunan zaɓe a jihohin guda biyu inda za a sake zaɓen gwamnoni.

A yanzu dai ƙidayar kwanaki ne kawai kafin ranar gudanar da zaɓen kujerar gwamna a wasu jihohi biyu na Najeriya da suka haɗa da Bayelsa da Goki,kuma tuni manyan Jam'iyyun da za su fafata da juna suka yi nisa wajen yin yaƙin neman zaɓen domin ganin sun kai ga nasarar kafa gwamnati,a yayin kuma da hukumar zaɓen INEC,musamman a jihar ke nuni da cewar ko da yake akwai ɗar-ɗar a game da yadda 'yan siyasar Jihar ta Bayelsa ke taƙale-taƙalen tada hankula,ita dai ta kammala shirin tinkarar zaɓen.

Gangamin yaƙin neman zaɓe ya kankama a jihohin

Tuni dai 'yan Siyasar Bayelsa,da ke da jam'iyyu daban- daban,musamman PDP da APC su ka yi nisa wajen ci- gaba da haɗa gangamin tarurruka a sassa daban-daban na jihar ,domin ganin sun samu nasara a zaɓen kujerar gwamna da za a gudanar a ranar 5 ga watan Disamba mai zuwa.Zaɓen dai na jihar Bayelsa,zaɓe ne da ke ɗaukar hankula matiƙa bisa ma la'akkari da cewar jihar tsohon shugaban Najeriya Dr Good Luck Jonathan ce,sannan kuma da maidakinsa Patience Jonathan ita ma ta yi dumu- dumu a harkokin Siyara.

Barazanar samun tashin hankali a zaɓen na ƙaruwa

Yanzu dai Mr Seriake Dicksen na PDP da ke san komawa kan mulkin jihar ta Bayelsa,zai fafata ne musamman da tsohon gwamnan jihar Chif Timiprye Sylva da zai takara a jam'iyyar APC,kuma ga dukkanin alamu yanayin siyasar ya zafafa matiƙa.Tun dai kafin wannan lokaci da ake ciki,akwai kashe-kashe da jikkata da suka afku,da kuma ake dangantawa da adawar siyasa a jihar.

Sauti da bidiyo akan labarin