Yunkurin neman mafita ga rikicin Libiya | Labarai | DW | 14.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunkurin neman mafita ga rikicin Libiya

Amirka da Italiya sun sabunta kira ga bangarorin da ke gaba da juna a Libiya da su ajiye makamansu tare da marawa shirin zama lafiya da Majalisar Dinkin Duniya ta tsara.

Wannan kiran dai ya zo ne a yayin da ministoci daga kasashe 20 suka halarci wani taro a birnin Rome na Italiya a karshen mako da nufin kawo karshen tashin hankulan da ake fama da shi a Libiya, tun bayan kifar da gwamnatin marigayi tsohon shugaban mulkin kama karyar kasar Moammar Gadhafi a shekara ta 2011.

A jawabin da ya yi sakataren harkokin kasashen ketare na Amirka John Kerry ya ce tilas ne bangarorin biyu su hakura su kafa gwamnatin hadin kan kasa domin kaucewa yiwuwar yin tasirin kungiyar IS a Libiyan, inda ya ce:

"Ba zamu bari halin da ake ciki a Libiya ya ci gaba da tafiya a haka ba. Hadari ne ga dorewar Libiya kana hadari ne ga al'ummar Libiya. Kasancewar a yanzu hare-hare kan 'yan kungiyar IS a Siriya da Iraki na tilasta musu yin hijira zuwa Libiya. Hadari ne ga kowa."