1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yuganda: Tsarin kula da 'yan mata na karkara masu al'ada

Mouhamadou Awal Balarabe
April 14, 2017

'Yan mata da ke rayuwa a karkara na ci gaba da kaurace wa makarantu sakamakon rashin samun sukunin kula da kansu a lokacin da suke ganin jinin haila na wata-wata a kasar Yuganda.

https://p.dw.com/p/2bFWb
Rashida Nalukenge links und Catherine Nantume rechts basteln Binden
Hoto: DW/S.Schlindwein

Da zaran an buga karaurawa da ke nuni da kawo karshen darusa a makarantar CARE da ke wata unguwar 'yan rabbana ka wadatamu a Kampala babban birnin kasar Yuganda, maimakon 'yan makarantar mata su koma gidan iyayensu, su na halartar kwarya-kwaryar horo na dinkin kunzugu ko audugar da mata ke amfani da ita a lokacin da suke al'ada ta wata-wata. Sadate Nduhira mai shekaru 27 da haihuwa ne ke koyar da su dabarun samar da audugan cikin sauki, saboda ta fuskanci wannan matsala a cikin kuruciyarta a kauyensu.

Kokarin rike 'yan mata a cikin makarantu a Yuganda

Schuldirektorin Sarah Nakabira und Künsterl Sadat Nduhira
Hoto: DW/S. Schlindwein

"Wannan dauri zai iya tsotse jinin na al'ada. Ana samar da shi ne daga tsohon tawul tare da hadashi da auduga. Wannan tsarin ya fi kunzugu da 'yan mata ke amfani da shi, saboda shi ana iya wankeshi, a busar, sannan a alkinta domin kashe kwayoyin cutar da ke ciki. Sannan a sa a wani kebebben wuri domin ya kasance a kowani lokaci cikin tsabta."

Kusan dai Euro biyar ake kashewa don samar da wannan audugar ta kayan al'adar mata, kudin da ba safai iyalan da ke rayuwa a unguwar ya ku bayi na kampala ke samu ba. Alhali wani bincike da hukumar UNUESCO ta gudanar ya gano cewar 'yan mata daya daga cikin 10 na kaurace wa aji a Yuganda a lokacin da take al'ada ta wata. daya daga cikin wannan hali itace Catherine Nantume mai shekaru 14 da haihuwa. tana shakkar zuwa aji a lokacin al'ada saboda ba ta so sauran dalibai suga jini na zuba a jikinta saboda ba ta da kudin sayan audugar al'ada ta mata.

Koyar da 'yan matan karkara hanyoyin kula da kansu

Schuldirektorin Sarah Nakabira und Künsterl Sadat Nduhira
Hoto: DW/S. Schlindwein

"A ko da yaushe ina fashin karatu, lamarin da ke jefani cikin wani hali saboda ina zama a gida ba tare da yin komai ba. na yi murna da wannan horo da ake bamu, ina koyan yadda zan samar da audugan al'adta da kaina. Yanzu mu ke rarraba wa wasu 'yan mata a makaratu a kyauta. a wasu lokutan ma mukan nunamusu yadda za su yi amfani da shi."

Batun na al'adar ta mata da kuma audugan da suke amfani da ita, na janyo muhawara a tsakanin 'yan Yuganda har ma a kafofin sadarwa na zamani irinsu facebook ko kuma a majalisar dokokin kasar. Shugaban Museveni ya yi alkawari a yakin neman zabe na shekarar da ta gabata cewar zai taimaka wa mata kan wannan batu, lamarin da ya jawo masa dimbim kuri'u daga iyayen yara. Ya ma nada mai dakinsa Janet Musveni a mukamin ministar ilimi don ta kula da wannan batu. sai dai ta ce ma'aikatarta bata da isashen kudin aiwatar da wannan alkawari. Saboda haka ne mai fafutukar kare hakkin mata Stella Nyanzi ta kaddamar da wani fadakarwa a kafofin sadarwa na zamani, lamarin da ya sa ta samu kudin samarwa yaran matan auduguar al'adar mata.