Yiwuwar barkewar sabon rikici a Ukraine | Labarai | DW | 10.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yiwuwar barkewar sabon rikici a Ukraine

Rahotanni daga Ukraine na nuni da cewa jerin gwanon motocin yaki sun doshi yankin gabashin kasar da 'yan aware ke iko da shi, a dai-dai lokacin da ake jin barin wuta a yankin Donetsk.

Wannan dai ya sanya Amirka nuna fargabar sake kazanacewar al'amura a wannan yanki, tana mai gargadin 'yan tawayen da cewa duk wani yunkuri da suka yi na sake kwace iko da wasu yankuna zai sabawa ka'idojin yarjejeniyar tsagaita wutar da suka cimma da bangaren gwamnatin Kiev. Dakarun sojin Amirka sun ruwaito cewa an gwabza kazamin fada tsakanin bangarorin biyu a kusa da filin sauka da tashin jiragen sama na Donetsk. Ita ma dai a na ta bangaren, kungiyar tsaro da hadin kan Turai OSCE ta nuna damuwarta yayin da ta ga motocin yaki na dosar yankin gabashi da 'yan aware ke da karfi.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman