Yin Allah wadai kan harin Potiskum | Labarai | DW | 10.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yin Allah wadai kan harin Potiskum

A wata sanarwa da fadar shugaban kasar Najeriya ta fitar, shugaban ya yi Allah wadai tare da alkawarin cewa gwamnatinsa za ta kama duk mai hannu cikin lamarin.

Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya yi tir da harin da aka kai a safiyar wannan Litinin a wata makarantar sakandare da ke birnin Potiskum na Jihar Yobe, harin da ya yi sanayiyar rasuwar dalibai kusan hamsin, tare da jikata wasu kusan 80.

Cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, shugaban na Najeriya ya ce komai dadewa, gwamnatinsa ta yi alkawarin kama duk wanda ke da hannu cikin wannan lamari tare da hukunta shi. Harin dai ya zo ne bayan fitar da wani sabon faifan bidiyo da kungiyar ta Boko Haram ta yi, inda a ciki shugaban kungiyar ke ba da tabbacin ya kafa Khalifa a yankunan da a halin yanzu ke karkashin kulawar su.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita Suleiman Babayo