1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaɗuwar ɓarɓashin nukiliya a Japan

March 27, 2011

Bincike ya gano lunlukawar sinadarin nukiliya a cikin ruwa da sararin iska a yankin Fukushima na ƙasar Japan

https://p.dw.com/p/10iEQ
Hoto: AP

Mahukunta a ƙasar Japan sun ɗauke ma'aikata dake aiki a tashar nukiliya ta Fukushima, bayan da suka gano tarin sinadarin nukiliya wanda ya tsiyayo daga tukunyar sarrafa dagwalon makamashin nukiliya ta biyu. Kamfanin samar da lantarki na birnin Tokyo ya sanar da cewa yawan sinadarin da aka gano a tashar ta nukiliya ya rumɓinya har sau miliyan goma bisa ƙa'iada, abinda ke nuni da cewa tukwanen sun samu mummunan lahani.

Ɓarɓashin nukiliyan da aka gano a cikin teku da ke kusa da tashar nukiliyan, shima ya haura mizani har sau 1,800. Alƙaluman hukama kan yawan waɗanda suka mutu sakamakon gigizar ƙasar ta Japan, yanzu ya kusan 10,500 yayin da wasu mutane kimanin 10,700 suka ɓace.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Yahouza Sadissou Madobi