Yawan wadanda suka mutu a fashewar wasu abubuwa a China ya karu | Labarai | DW | 13.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yawan wadanda suka mutu a fashewar wasu abubuwa a China ya karu

Mahukunta a birnin Tianjin sun ce fashewar abubuwa da kuma gagarumar gobara da ta tashi ta kuma haddasa babbar asara.

An tabbatar da mutuwar akalla mutane 50 sannan 701 sun samu raunuka, 71 raunuka masu tsanani a fashewar wasu abubuwa a birnin Tianjin mai tashar jirgin ruwa a kasar China. Mahukunta a birnin sun ce fashewar abubuwa da kuma gagarumar gobara da ta tashin ta kuma haddasa babbar asara. Wani faifayen bidiyo ya nuna yadda harshen wuta ya mamaye sararin samaniyar birnin.

A ranar Laraba da dare an kira 'yan kwana-kwana lokacin da gobara ta tashi a wani wurin ajiye kaya da suka hada da sinadarai masu guba a tashar jirgin ruwa. Amma sai kwatsam wasu abubuwa masu yawa suka fara fashewar lokacin da masu kashe gobarar suka isa wurin, sun kuma rasa akalla ma'aikatansu su 12.