Habakar yawan jam'iyyun siyasa a Najeriya
June 21, 2018Ya zuwa yanzu dai akwai jam'iyyu dai dai har 68 da ke fatan taka rawa a cikin zaben tarrayar najeriya na watan Fabrairun shekarar badi. To sai dai kuma sama 136 ne dai ke layi kuma ke jiran samun rijistar kuri'a a wani abun da ke shirin kafa tarihi na yawan jam'iyyu a cikin fagen siyasar Najeriya.
Ko bayan nan dai a fadar hukumar INEC din ana sa ran karin masu kada kuri'ar ya zuwa mutane kusan miliyan 80 daga 60 din da suka shiga cikin shirin a shekarar 2015.
Tuni dai yawan jam'iyyun ya fara tada hankali cikin kasar inda ilimin zaben ke da karanci sannan kuma mutuwa ko yin rai a cikinsa ke kara yawa.
Dr Umar Kari dai na zaman wani mai sharhi a cikin harkoki na siyasa ta kasar, kuma a fadarsa ko bayan rudani ga alamomin jam'iyyun ana kuma iya fuskantar bacin kuri'u yayin zaben da yan kasar ke yi wa kallo da idanu na basira. Kuma a fadar Malam Aliyu Bello dake zaman kakaki na hukumar zaben, INEC tana tunanin samo hanyar tunkarar lamuran da a cewar sa ke tafiya a bisa dokoki na kasa.