1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Yawan al'umma a Afirka sun dauki hankalin jaridun Jamus

Abdullahi Tanko Bala MA
August 13, 2021

Yawan al'umma a Afirka na bunkasa cikin hanzari; sai dai kuma abin tambayar shi ne ko adadin jama'ar zai iya rubanyawa nan da shekara ta 2050? Ga fahimtar jaridun na Jamus

https://p.dw.com/p/3yxBJ
Weltzeit | Traffic Jam in Lagos, Nigeria
Hoto: Adeyinka Yusuf/AA/picture alliance

Jaridun sun yi waiwaye inda suka ce a shekarar 1948 yawan al'ummar Afirka ba su wuce miliyan 200 ba, sai dai kuma al'amura da dama sun sauya tun daga wancan lokaci. A cikin shekaru takwas yawan jama'ar ya kai biliyan daya da miliyan 300 a yau, ninkin yawan jama'ar da ke nahiyar Turai. Babu wata nahiyar da jama'arta ke bunkasa haka kamar Afirka. A cewar masana kididdigar jama'a, yawan al'ummar na iya sake rubanyawa nan da shekarar 2050. Zuwa wannan lokaci yawan jama'ar Turai baki daya zai kasance daidai da yawan jama'ar Najeriya.

Shin ana iya cewa wannan matsala ce gawurtacciya da ke tunkarar nahiyar? Kuma shin tana iya tasiri a kan tattalin arziki? Wannan babu ko tantama karuwar bunkasar jama'a na da tasiri da kuma irin nasa hadari. 

A wasu wurare yawan jama'ar na iya haifar da matsalolin tattalin arziki da na siyasa. Ana iya ganin wannan zahiri ne a yankin Sahel, misali an fi haihuwa a yankin fiye da kowane yanki a duniya, sannan kuma yankin na fama da karancin albarkatun kasa. Ko da yau yawan jama'ar na taimakawa wajen yaduwar rigingimu. Saboda haka meine ne abin yi yadda bunkasar jama'ar ba za ta zama wata gawurtacciyar matsala ba ga Afirka?

Nigeria Kinder
Hoto: Imago Images/Zuma

A sahun gaba dai shi ne inganta Ilimi a matakin farko musamman ilmin ’ya‘ya mata. Wannan mataki ba ma kawai yana da muhimmanci ba ne ga tattalin arziki, yana daya daga cikin hanyoyi masu nagarta na rage yawan haihuwa saboda matan da ba su yi karatu ba su kan yi aure da wuri tare da haihuwar ‘ya’ya da yawa.

Abu na biyu shi ne samun aiki. Matasan Afirka fiye da miliyan daya ne ke fita neman aiki a kowane wata domin samun abin da za su rike kansu, amma ba dukkan su ne ke iya samun aikin ba. Haka matsalar ke zagawa zuwa al'umma ta gaba.

Za a mika tsohon shugaban Sudan Omar al Bashir ga kotun kasa da kasa dake Hague. Wannan shi ne taken sharhin jaridar die tageszeitung da kuma Frankfurter Allgemeine Zeitung

Tsawon shekaru 12 kotun shari'ar mayan laifuka ta duniya ICC ta bada sammacin kama Omar al-Bashir akan tuhumar kisan kare dangi da cin zarafin al'umma a Dafur. A yanzu dai gwamnatin rikon kwarya ta Sudan ta yanke shawarar mika tsohon shugaban mai shekaru 77 a duniya wanda ya shafe shekaru 30 yana mulkin kasar ga kotun ta kasa da kasa da ke Hague kamar yadda ministar harkokin wajen Sudan Mariam al Mahdi ta shaidawa kamfanin dillancin labaran kasar.

Sudan Khartum | Ex-Präsident Umar al-Baschir vor Gericht
Hoto: Getty Images/AFP/E. Hamid

Wannan dai ya biyo bayan ziyarar da babban mai gabatar da kara na kotun ta ICC Karim Khan ya kai ne zuwa Sudan. Gwamnatin Sudan din dai ta yi alkawarin ba da cikakken goyon baya ga kotun ICC. Sai dai ko meine ne makomar al Bashir a yanzu? Ko yaya za ta kaya zai dade kafin tsohon shugaban mai shekaru 77 a duniya ya sami yanci.

A nata sharhin jaridar  Süddeutsche ta yi tsokaci a kan sabuwar kwayar cutar Marburg wadda ke da matukar hadari da kuma yaduwa. Kawo yanzu dai hukumomi sun tabbatar da cewa mutum guda ya kamu da cutar a kasar Guinea da ke yammacin Afirka watanni biyu bayan kawo karshen annobar Ebola a kasar.

Cutar wadda ke kama da Ebola da ake samu daga jemage yana sa zazzabi mai zafi da kuma kumewar jini a jiki. Cutar na yaduwa ta hanyar haduwar jiki da kumashafar gumin jikin mutum.Ya zuwa yanzu dai babu wani magani da aka gano na yaki da cutar.

Hukumar lafiya ta duniya WHO na gudanar da bincike bayan samun rahoton bullar cutar a kan iyakar kasashen Saliyo da Liberia.