Yarjejeniyar zamna lahia tsakanin gwamnati da yan tawayen gabacin Sudan | Labarai | DW | 10.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yarjejeniyar zamna lahia tsakanin gwamnati da yan tawayen gabacin Sudan

Gwamnati da yan tawayen gabacin Sudan, sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar tsaigaita wuta, a birnin Asmara na ƙasar Erythrea.

Saidai ya zuwa yanzu, ba a bayyana matakan da wannan sulhun ya tanada ba.

Tun watan satumber da ya wuce, ɓangarorin 2, su ka cimma daidaito, a kan batun ajje makamai, tare da alƙawarta ci gaba da tantanwa, domin kawo ƙarshen rikicin ,da ya ɗauki tsawn shekaru 10.

Sakatare Jannar na rundunar yan tawayen gabacin Sudan, Mubarack Mubarack Salim, ya shaidawa manema labarai cewa, yarjenejiyar ta tadani saka kuɗaɗe masu yawa, domin kyautata rayuwar al´umomin yanki gabas, da ke fama da ƙazamin talauci.