1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiLatin Amurka

Yarjejeniyar kasuwancin bai daya mafi girma

Suleiman Babayo ZMA
January 9, 2026

Brazil ta yi maraba da yadda galibin kasashen Turai suka amince da yarjjeniyar kasuwancin bai daya da wasu kasashen Latin Amurka.

https://p.dw.com/p/56bpq
Yarjejeniyar kasuwancin Turai da kasashen Latin Amurka
Yarjejeniyar kasuwancin Turai da kasashen Latin AmurkaHoto: Matilde Campodonico/AP Photo/dpa/picture alliance

Shugaba Luiz Inacio Lula da Silva na kasar Brazil ya yi maraba da matakin kungiyar kasashen Tarayyar Turai na amincewa da yarjejeniyar kasuwan ta bai daya da wasu kasashen yankin Latin Amurka. Shugaban ya bayyana haka a sakon da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na zamani.

Tasirin yarjejeniyar

Kasasshen Kungiyar Tarayyar Turai sun nuna amince da yarjejeniyar kasuwancin bai daya da kasashen na Brazil, da Ajentina, da Uruguay gami da Paraguay, kamar yadda tun farko Kamfanin dillacin labaran Jamus, DPA ya ruwaito majiyoyin diflomasiyya.

Shi dai wannan sabon tsarin kasuwancin bai daya zai hada mutane fiye da duk sauran tsare-tsaren kasuwancin kasuwanci na bai daya inda zai zama mafi girma a duniya.

Fara aiki da wannan sabon tsarin zai janyo kayayyaki amfanin gona na kasashen kudancin Amurka da ke da arha, su samu kasuwa tsakanin kasashen kungiyar Tarayyar Turai.