Yarjejeniya kan shirin nukiliyar Iran | Labarai | DW | 03.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yarjejeniya kan shirin nukiliyar Iran

Shugabannin kasashen duniya da Iran sun cimma kwarya-kwaryar matsaya da za ta kai ga samar da yarjejeniya dawamammiya kan shirin nukiliyar Iran.

Kantomar harkokin waje ta kungiyar kasashen Turai ta EU Federica Mogherini ce ta ambata hakan a birnin Lausanne na kasar Switzerland bayan kammala kaiwa ga wannan gaba, inda ta ke cewar hakan babban cigaba ne kuma daga nan zuwa watan Yunin da ke tafe ne za a karkare komai.

Shugaban Amirka Barack Obama ya jinjinawa wannan matsayi da aka kai, inda ya ke cewar Amirka da kawayenta da kuma kasar ta Iran sun fahimtar juna da ke ciki da dimbin tarihi.

Ita kuwa Isra'ila cewa ta yi tana adawa da wannan matsaya da aka cimma inda firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya ce zai kira wani taro na majalisar ministocin kasar don tattaunawa kan lamarin.