′Yan tawayen Siriya sun harbo jirgin sojoji | Labarai | DW | 11.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan tawayen Siriya sun harbo jirgin sojoji

Gamaiyar kungiyoyin 'yan tawaye sun kakkabo wani jirgin yakin sojojin gwamnatin Siriya, da ke shawagi a kusa da lardin Sweidea da ke ckin yankunan da aka cimma tsagaita wuta.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama da ke sa'ido a Siriya, sun tabbatar da ganin guraguzan jirgin bayan da 'yan tawayen suka fidda sanarwar daukar alhakin harbo jirgin. To sai dai kungiyoyin sun kuma bada tabbacin jin karar harbe-harbe dake nuna alamun ci gaba da gumurzun wuta tsakanin 'yan tawayen da dakarun gwamnati a tsaunuka da ke kan iyakan da Damascus a wannan wannan Talata.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da sojojin da ke samun goyo bayan dakarun Amirka a Siriyar, ke ikirarin kwace wani yanki da dake zama sansanin IS na samun horo, sansanin da ke kusa da babar cibiyar mayakan dake arewacin Siriya wato Raqa.