1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanci

'Yan ta'adda sun lalata motoci a Monguno

November 11, 2022

Kazamin hari da mayakan ISWAP suka kai kan 'yan agaji a Monguno na jihar Bornon Najeriya ya haifar da lalata motoci guda 22 da ake aikin jin kai da su. Sannan ana zargin mayakan da tafiya da wasu motocin jami’an tsaro.

https://p.dw.com/p/4JO6E
'Yan ISWAP sun saba lallata motoci a hare-harensu a jihar BornoHoto: AFP/A. Marte

Da tsakiyar dare ne mayakan ISWAP suka afka wa garin na Monguno cikin motocin yaki da babura inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi tare da wucewa kai tsaye zuwa ofisoshin Kungoyoyin da ke aikin jin kai a yankin. Wani mazunin garin Munguno na jihar Bornon Najeriya da ya nemi in sakaye sunan sa saboda dalilai na tsaro ya ce: " Mun ta jin harbe-harbe da kabbara kuma da muka fita da safe mun ga kone-konen motoci da suka yi, kuma gidan tsohon Chairman ma, an zo an kona amma salwantar rayuka dai kam ba mu ga ko daya ba” 

Rahotanni sun nuna cewa ganin 'yan bindiga ba su samu ma'aiakatan da ke gudanar aikin jin kai a wannan ofisoshin ba, sai suka cunna wuta kan motocin da ke harabar ofisoshin tare da nemen tafiya da wasu. Daga cikin motocin da aka kona har da motocin alfarma da ake kira SUV a takaice da kuma motocin da ake aikin raba abinci da sauran kayan jin kai tsakanin ‘yan gudun hijira a Monguno da sauran yankuna.

Nigeria | Löscharbeiten in Auno nach Brandanschlag
Motocin da ke dakon kayan agaji ma ba sa tsira daga hare-hareHoto: Getty Images/AFP/A. Marte

Ba a samu asarar rai a harin ba

Babu wani rahoto da ya nuna cewa an samu asarar rai a wannan hari wanda ya firgita al'umma da suka saki jiki saboda fara wanzuwar zaman lafiya a yankin Arewa maso gabashin Najeriya. Masu aikin jin kai sun bayyana fargabar cewa za a samu koma-baya a aikin jin kai a wannan yanki. Tuni wasu daga cikin ma'aikatan jin kan suka tsere daga yankunan musamman ganin Kungiyoyin ISWAP da Boko Haram na farautarsu.

Sama'ila Idris Hinna da ke aikin jin kai a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya ya ce wannan hari zai shafi ayyukan taimakawa wadanda rikicin Boko Haram ya shafa. Ya ce: " Wuri ne da ya ke dauke da mata da kananan yara da yawa wadanda suke bukatar taimako na magunguna da taimako na abinci da sauran kayan al'amuran yau da kullum. Saboda haka wannan abin da ya faru zai matukar kawo ci baya kuma zai matukar kawo illa sosa.”

Hannun agogo ya koma baya a yaki da tarzoma

Masu fashin baki kan harkokin tsaro na da irin kallon da suke wa harin.  Bakuros Baraden Tikau na jihar Yobe ga misali ya ce: " Wannan wani kalubale ne musamman ma yadda aka tinkaro Kakar zabe a wannan kasa ta mu Najeriya sanna kuma ta nuna cewa har yanzu akwai sauran Rina a kaba a kan harkar tsaro musamman a Arewa maso gabashin Najeriya.”

Nigeria Maiduguri Boko Haram
Jami'an tsaro na tsayuwar daka wajen dakile hare-hare a BornoHoto: picture-alliance/dpa

Jami'an tsaron Najeriya sun ce sun dakile wannan hari tare da fatattakar mayakan na ISWAP, lamarin da ya hana mayakan yin katabus. Wannan hari da ke zuwa a daidai lokacin da ake samun nasarar a kan mayakan ISWAP da Boko Haram a kusan dukkanin sassan Arewa maso gabashin Najeriya, ya zama Kalubale ga rundunar sojojin Najeriya.

Sai dai shugaban rundunar Janar Faruq Yahya ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba duk nasarorin da suke samu. Ya ce: "Idan ana samun nasara, ba ya nuna shi ke nan a zauna haka ba, dole ne a tsaya a kara jaddada ayyuka. Abin da da dan ta'adda mai bindiga guda daya zai yi na tada hankali na da yawa. Ka ga kenan don samu nasara, kamata ya yi a kara kaimi. ”

Al'ummar garin Mungono na ci gaba da gudanar da rayuwar cikin kwanciyar hankai inda aka shaida ganin karuwar matakan tsaro a yankuna don tabbatar da cewa harin bai sake faruwa ba.