1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Shi'a na shirin sulhu da gwamnatin Najeriya

Abdoulaye Mamane Amadou
October 19, 2019

Kungiyar mabiya Shi'a a Najeriya ta bayyana matsaya kan matakin shiga sulhu da hukumomin Najeriya domin shimfida zaman lafiya da kawo karshen fitina tsakaninta da hukumomin kasar.

https://p.dw.com/p/3RZkw
Nigeria Anhänger von Schiiten-Führer Ibrahim Zakzaky
Hoto: AFP/S. Adelakun

Kungiyar mabiya Shi'a a Najeriya ta ce tana shirye da ta zauna da gwamnatin kasar don sasantawa a wani yunkuri na samun zaman lafya tsakaninta da gwamnati. 

Shugaban kungiyar na riko a kasar Shekh Yakubu Yahaya Katsina ne ya bayyana haka ga manema labaru a Katsina. inda ya ce kuniyar ta shirya duk wata tattaunawa da gwamnati ba tare da wani sharadi ba muddin gwamnatin ta Najeriya na bukatar hakan.