′Yan sandan Najeriya sun ɓace | Labarai | DW | 24.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan sandan Najeriya sun ɓace

Rahotanni daga Najeriya na nuni da cewar kimanin jami'an 'yan sandan ƙasar 35 ne suka yi ɓatan dabo a yankin arewa maso gabashin ƙasar.

Wannan dai ya faru ne bayan da Ƙungiyar Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai a yankin arewa maso gabashin ƙasar ta kai farmaki a makarantar horar da 'yan sanda da ke garin Gwoza a jihar Borno. Rundunar 'yan sandan ƙasar ta sanar da cewar wannan shi ne karo na uku da ƙungiyar ke kai mata farmaki cikin wannan wata na Agusta a jihar ta Borno da ke yankin arewa maso gabashin ƙasar da yake fama da rikici. Tuni dai sabon shugaban 'yan sandan ƙasar Suleiman Abba ya umurci da a tsaurara matakan tsaro a yankin.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hasane