1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

'Yan sandan Isra'ila sun kai samame ofis din Al Jazeera

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
May 5, 2024

Wani faifan bidiyo ya nuna jami'an tsaron cikin fararen kaya suna lalata naurorin daukar hoto na Al Jazeera a Otal din

https://p.dw.com/p/4fWkB
Hoto: Mahmoud Ibrahem/Anadolu Agency/picture alliance

'Yan sandan Isra'ila sun kai samame Otal din da gidan talabijin din Al Jazeera ke amfani da shi a gabashin birnin Jerusalem a matsayin ofishinsa na yada shirye-shirye, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya tabbatar a Lahadin nan.

Karin bayani:Al Jazeera ta kai Isra'ila kotun ICC

Wani faifan bidiyo da ya karade shafukan Intanet, ya nuna jami'an tsaron cikin fararen kaya suna lalata naurorin daukar hoto na Al Jazeera a Otal din, biyo bayan umarnin majalisar ministocin firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na haramtawa Al Jazeera yada shirye-shirye a kasar, sakamakon zargin zama barazana ga tsaron kasar.

Karin bayani:Zargin sojojin Isra'ila da kisan Shireen

Gidan talabijin din na Al Jazeera ya musanta zargin zama barazanar tsaro ga Isra'ila, yana mai cewar labari ne maras tushe balle makama, kuma wannan wani yunkuri ne kawai da Isra'ila ke yi wajen kara jefa rayuwar 'yan jarida cikin hatsari.

Kafar yada labaran Al Jazeera ta yi kaurin suna wajen sukar yakin da Isra'ila ke yi a Gaza, kuma tana ci gaba da yada labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa game da yakin, ba dare da rana.