1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Akleh: Al Jazeera ta kai Isra'ila kotun ICC

December 6, 2022

Wata sanarwar da tashar Al Jazeera mallakin kasar Katar ta fita ta ce gidan talabijin din ya samu wasu sabbin hujjoji da ke tabbatar masa cewa sojojin Isra'ila ne suka bindige 'yar jaridar.

https://p.dw.com/p/4KYJV
Hoto: Al Jazeera Media Network/AP/picture alliance

Gidan Talabijin na Al Jazeera ya shigar da kara a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ICC, a birnin Hague a kan kisan da aka yi wa 'yar jarida  Shireen Abu Akleh. A cikin takardun shigar da kara da gidan talabijin din ya shigar a  wannan Talatar ya ce sojojin Isra'ila ne suka halaka 'yar jaridar a yayin da take tsaka da aiki.

A ranar 11 ga watan Mayun wannan shekara ne dai aka halaka 'yar jaridar a yayin da take tsaka da aiki a yankin yamma da kogin Jordan.