′Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a Hong Kong | Labarai | DW | 26.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a Hong Kong

Wata kotu a Hong Kong ta ba da umarni ga jami'an tsaron da su kori jama'ar da suka mamaye wani dandalin.

An yi taho mu gama tsakanin 'yan sanda da masu yin bore a Hong Kong a lokacin da masu ɗamara suka durfafi jama'ar da suka datse wani dandalin, wanda wata kotun ta ba da umarnin korar jama'ar da ke yin zaman dirshan a kansa.

'Yan sandan sun kama mutane kusan guda 80 a ciki har da wasu shugabaniin ɗaliban guda biyu masu fafutukar neman sauyi na demokaraɗiyya a Hong Kong ɗin.