′Yan sanda a kasar Indiya sun tarwatsa masu zanga-zanga a yakin Kashmir | Labarai | DW | 25.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan sanda a kasar Indiya sun tarwatsa masu zanga-zanga a yakin Kashmir

Hukumomin Indiyan yanzu haka sun haramta yin amfani da wayoyin tafi da gidan ka don aikewa da sakonnin yanka Shanu a yankin.

'Yan sanda a kasar Indiya sun yi amfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsa wasu gungun mutane da ke gudanar da wata zanga-zanga don nuna kin jinin gwamnatin kasar Indiya. 'Yan sanda a kasar Indiya sun yi amfani da barkonon tsohuwa don tarwatsa masu zanga zangar a yankin Kashmir da ke bangaren yankin Kasmir.

Wani dan sandan kasar Indiyan ya fadawa manema labarai a yau jumma’ar nan cewar masu zanga -zangar na kada tutoci kasar Pakistan da kuma tutar mayakan sa kai gami da jefa duwatsu akan jami’an tsaron gwamnatin Indiyan, a dai dai lokacin da ke suke kokarin hanasu zanga- zangar a Srinagar tare da Karin wasu gurare biyu a yakin.