′Yan makaranta na yaki da cin zarafi | Himma dai Matasa | DW | 16.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

'Yan makaranta na yaki da cin zarafi

A kasar Afirka ta Kudu ana samun matasa da ke tashi tsaye domin yaki da cin zarafin da ake samu, domin kyautata makomarsu.

Sanelisiwe Dick tana kawo sauyi ta wannan fanni ta wajen yadda take rayuwa, inda tare da taimakon wata kungiya mai zaman kanta 'yar shekaru 17 da haihuwar suke gayyatan 'yan makaranta zuwa wani shirin kara wa juna sani a yankin Nalson Mandela Bay.

Sanelisiwe Dick 'yar shekara 17. 'Yar Afirka ta Kudun ta sadaukar da kai bisa yaki da cin zarafi a yankin Nelson Mandela Bay. Kowani mako 'yar makarantar tana ziyartar kabarin kawarta Cindy, wadda aka yi wa fyade kuma aka kashe shekara guda ke nan. Ga abin da take cewa lokacin da ta kai ziyarar:

"Ya kasance abu mai cike da tantanma, farkon zuwa bayan binnewar. Lokacin na kadu na ji wani iri, saboda ba mu yi tsammani ba. Na yi tunani yanzu ta tabbata ba za mu sake ganin Cindy ba. Mai yiwuwa sai a lahira."

Rashin aikin yi ya katutu a yankunan marasa galihu

Sanelisiwe Dick tana rayuwa a garin Walmer na marasa galihu, wadanda rashin aiki ya yi wa katutu. Tashin hankalin bai wai da matasa kadai ya ke ritsawa ba, su ne ma suke aikatawa, kuma tare da sauran matasan suna ganin akwai abin da za su iya:

"Saboda da yawa suna aiki da gungun masu aikata laifuka, sai ka yi duk wani abu maras kyau domin ka saje. Rashin aiki yana taka rawa da talauci amma babba abun shi ne matsin lamba daga abokai"

Tare da saura, Sanelisiwe ta fara wani shiri domin saka matasa tunanin hanyar gina al'uma na gari. Kungiyar Masifunde mai zaman kanta tana horas da su, kuma tana tallata shirin. Linda Zali ta kungiyar Masifunde ta bayyana abin da yasa aka zabi wadanda za su gabatar da shirin wa magajin gari:

"Akwai dalilin da ya sa kuke kwamitin. Muna dakarfin gwiwa a kan ku."

Saneliswe ta fadi abin da ke kara mata karfin gwiwa:

"Mun gaji da zama wadanda aka cutar. Lokaci ya yi da za mu dauki makomar rayuwarmu. Muna cikin matsalar kuma muna cikin mafita."

Akwai shirye-shiryen inganta muhalli

Sanelisiwe Dick tana son matasa su dauki nauyi- da inganta lafiyar muhalli kamar gyara azuzuwan makaranta da suka lalace. Sun gabatar da taswirar shirin ga magajin gari, ga abin da take cewa lokacin:

"Yanzu abu na farko kowa ya ba da taimakon gyara yanayi. Mutane suna tunanin aikin gwamnati ne ko 'yan sanda sai dai nauyi a kan kowa."

Tare da sauran wanda suke aiki tare kungiyar Masifunde, tana son ganin matasan yankin Nelson Mandela Bay sun samu ta cewa a makomarsu.

Sauti da bidiyo akan labarin