1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan majalisa sun sake bijire wa Trump

February 12, 2019

Sanatoci a Amirka, sun cimma matsaya kan bai wa Shugaba Donald damar amfani da wasu kudade wajen gudanar da aikace-aikace.

https://p.dw.com/p/3DBY2
USA Krise Shutdown l Präsident Trump verkündet vorläufige Aufhebung der Haushaltssperre
Hoto: picture-alliance/CNP/O. Douliery

Gabanin cikar wa'adin iya sake fuskantar tarnaki a harkokin gwamnatin Amirka, Sanatocin jam'iyyun Republican da kuma na Democrats, sun cimma yarjejeniya kan bai wa gwammatin Shugaba Donald damar amfani da wasu kudade wajen gudanar da aikace-aikace.

Sai dai bayanai sun ce 'yan majalisar sun yi fatali da bukatar shugaban kasar na dala biliyan 5 da miliyan 700 da sunan gina ganuwa tsakanin Amirkar da kasar Mexico.

Babu dai tabbacin ko shugaban na Amirka Donald Trump zai amince ya sanya wa yarjejeniyar 'yan majalisar da suka cimma a daren da ya gabata, hannu.

Wannan batun ne ma ya janyo dakatar da ayyukan gwamnati a Amirkar na tsawon kwanaki 35 a makonnin baya, tsayuwar da ba a taba ganin irinta ba a tarihin kasar.