Yan fashi da makami sun addabi Zamfara | Siyasa | DW | 31.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yan fashi da makami sun addabi Zamfara

Saboda rashin tsaro a Najeriya ya sanya yan fashi da makami su kara yawan hare-haren su da kashe jama'a

Hukumomi a Jihar Zamfara dake arewacin Najeriya sun karfafa matakan tsaro,bayan da wasu mutane da ake kyautata zaton yan fashi ne suka kashe a kalla mutane kusan 20 a wani kauyen Kaboro a yankin Dan sadau na karamar hukumar Maru ranar Talata.

A ranar Talata ne dai gungun wadannan mutane da ake kyautata zaton yan fashi da makami ne suka aukawa kauyen Kaboro na Dansadau, inda suka kashe jama'a da dama ciki har da mai garin kauyen, a wani mataki da hukumomi da mutanen kauyukan suka baiyanashi a matsayin na fashi da makami, wanda dama suka gallabi al'uman yankin.

Rahotanni dai sun nuna cewa yan fashin sun kuma kona gawarwakin mutanen da suka kashe ta yadda ma ba'a iya gane wasun su. Wannan kisan da kuma harin dai yazo ne yan makwanni bayan harin da wasu gungun yan fashi suka kai a wani kauye dake karamar hukumar Birnin Gwari, inda nan ma suka kashe mutane kimanin 20. Tun bayan wancan hari ne hukumomi suke bayyana daukar matakan magance lamarin, wanda kuma harin na baya bayan nan a Zamfara ya saka ayar tambaya game da matakan da hukumomin ke dauka.

Nigeria Boko Haram Anschlag

Alamar hare-haren kungiyar Boko Haram

Koda yake nayi kokarin jin ta bakin hukumomin yan sanda a jihar ta Zamfara da kuma jami'an gwamnati, amma ba tare da samun nasara ba, acan bayan dai mai baiwa gwamnan jihar ta Zamfara shawara akan harkokin yada labarai, Sani Abdullahi Tsafe ya tabbatar mani ta wayar tarho kokarin da hukumomin jihar keyi na inganta tsaro:

"Gwamnatin Jihar Zamfara na iya bakin kokarin ta wajen zakulo wadanda keda alhakin kai wadannan hare-hare tare da taimakon jami'an tsaro da kuma jama'a, kuma ba zatayi kasa a guiwa ba wajen inganta tsaro a tsakanin al'umman ta."

Wannan dai ba shine karon farko ba da maharan ke kai makamancin wannan hari akan jama'a, tare kuma da kisa, a jihar ta Zamfara ba. Domin ko a watan Oktoba na bara da kuma watannin Janairun da Yunin bana ma, sai da yan fashin suka halaka jama'a da yawan su ya haura 40, a hare-hare guda uku, al'amarin da kuma ya sake dawo da batun kafa rundunonin yan sanda na jihohi a zukatan jama'a. Sai dai wani tsohon babban jami'in yan sanda, Alhaji Zubairu Jibia ya sheda mani cewar wannan ba itace mafita ba:

"A gaskiya wannan bashi bane mafita. Abin yi shine a kara yawan jami'an tsaro, domin yawan jami'an tsaro a kasa sunyi kadan, kuma a basu kayan aiki wannan itace mafita."

Goodluck Jonathan

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

To ko wane tabbaci hukumomi ke dashi ga jama'ar jihar ta Zamfara? Ga dai mai baiwa gwamnan jihar ta zamfara shawara akan harkokin yada labarai:

Sai dai kuma duk da wannan tabbaci daga bakin hukumomi, tuni dai yan arewacin kasar ke cewa sun gaji da gafara sa basu ga kaho ba, kamar yadda wannan malamin da baya so na anbaci sunan sa ke cewa.

Mawallafi: Babangida Jibril
Edita: Umaru Aliyu