′Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane a Mali | Labarai | DW | 07.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane a Mali

Har ya zuwa yammacin wannan Jumma'a, ba'a samu shayo kan matsalar 'yan ta'adda da suka yi garkuwa da wasu mutane a Hotel Byblos da ke birnin Sevare a Mali.

Tun dai da sanyin safiyar wannan Juma'a ce 'yan bindigar suka yi dirar mikiya a wannan Otel da akasari baki 'yan kasashen yamma ke sauka a cikinsa, inda kawo yanzu aka samu rasuwar mutane hudu, cikin su har da sojojin kasar ta Mali biyu, da kuma daya daga cikin maharan, sannan wasu sojojin na mali uku sun ji rauni. Wata majiya ta sojan kasar ta Mali ta ce sun harbe wani mutun da ke daure da jigidar bam, sannan kuma a kofar Otel din akwai gawar wani mutun jar fata a yashe, inda a cewar wata majiyar ta sojan kasar ta Mali, a kalla dai akwai baki yan kasashen waje biyar cikin Hotel din da suka hada da 'yan kasar Afirka ta Kudu guda uku, da dan kasar Faransa guda, kuma dan kasar Ukraine.