1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun kashe mutane 45 a jihar Kaduna

Zulaiha Abubakar
May 6, 2018

Akalla mutane 44 ne suka rasa ransu a kauyen Gwaska da ke jihar yayin da wasu dauke da makamai suka kai musu hari.

https://p.dw.com/p/2xGRq
Nigeria entführte deutsche Archäologen wieder frei
Hoto: picture alliance/AP Photo/L. Oyekanmi

Wannan kisan gilla ya biyo bayan mutuwar mutane 25 cikin wadansu hare-hare mabanbanta a arewacin Najeriyar cikin makon da ya gabata, a daidai lokacin da iyalan wasu mutane 13 ke cikin alhinin rashin su a jihar Zamfara sakamakon wani rikici tsakanin barayin shanu da kuma 'yan banga a Jihar Zamfara.

Yanayin tsaro dai na kara ta azzara a kasar lamarin da a halin yanzu ya haifar wa da shugaban kasar Muhammadu Buhari samun suka daga bangarori daban daban a ciki da wajen kasar. Bayan da matsanancin talauci ya addabi talakan kasar duk kuwa da cewar shugaba Buharin bai jima da bayyana aniyar sa ta sake neman takarar shugabancin kasar a shekara ta 2019 ba.