′Yan bindiga sun kashe mutane 30 a jihar Filato | Labarai | DW | 07.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan bindiga sun kashe mutane 30 a jihar Filato

Kimanin mutane 30 aka kashe, wasu 15 suka sami raunuka sanadiyyar wani hari da wasu mutane suka kai a ƙauyen Bachit na ƙaramar hukumar Riyom ta jihar Filato.

Rahotanni dai sun ce 'yan bindigar sun auka wa mazauna ƙauyen ne a jiya, inda suka kashe jama'a tare da ƙona gidaje da kuma rumbunan na abinci da dama.Wani da ya shaida faruwar lamarin Mr. Dong Audu, ya shaida wa wakilinmu na Jos Abdullahi Maidawa Kurgwi cewar mutanen yankin sun shiga halin ɗimuwa bayan faruwar harin.

Kakakin rundunar soji da ke wanzar da zaman lafiya a jihar Filato, Keftin Salisu Mustapha, yace an tura wasu ƙarin jami'an tsaro zuwa ƙauyen a daren jiya, domin su ƙaddamar da bincike da nufin gano maharan.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Abdourahamane Hassane