′Yan bindiga sun hallaka sojojin Najeriya hudu | Labarai | DW | 17.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan bindiga sun hallaka sojojin Najeriya hudu

Wasu 'yan bindiga sun yi wa sojojin Najeriya kwanton bauna a yankin Niger Delta inda suka hallaka sojojin guda hudu.

Harin na 'yan bindiga dai ya gudana ne a karamar hukumar Akuku da ke yankin na Niger Delta inda daga cikin sojojin hudu akwai wani babban Manjo guda na sojan Najeriya. Hakan dai na zuwa ne kasa da 'yan sa'o'i kafin zaben 'yan majalisun dokoki da za a yi a duk kananan hukumomin jihar a ranar Asabar.

Tuni dai dama ake zaman dar-dar dangane da matakan tsaro a wannan zabe, wanda gwamnatin kasar ta Najeriya ta ba da umarnin daukan kwararan matakai na ganin ya gudana cikin tsanaki.