′Yan bindiga sun hallaka mutane a Najeriya | Labarai | DW | 14.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan bindiga sun hallaka mutane a Najeriya

'Yan bindiga sun hallaka kusan mutane 30 a Jihar Plateau ta Najeriya

'Yan bindiga sun hallaka kimanin mutane 27 a garin Riyon da ke Jihar Plateau a yankin tsakiyar Najeriya, kamar yadda wasu jaridun ƙasar suka ruwaito a wannan Talata.

Kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA, ya ruwaito daga kafofin yada labaran Najeriya cewar, yayin harin an ƙona gidaje kusan 70, wanda harin ya tarwatsa fiye da mutane 3000. Jami'ai sun ce harin ya yi kama dana Ƙungiyar Boko Haram, wadda ta yi ƙaurin suna wajen tashin hankali a yankin arewacin ƙasar ta Najeriya tare da hallaka mutane.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Abdourahamane Hassane